logo

HAUSA

Ribar masana’antun Sin ta karu a watan Oktoba

2023-11-27 15:40:58 CMG Hausa

Jimillar ribar manyan masana’antun kasar Sin ta karu a karo na 3 a jere a watan Oktoba, inda ribar manyan masana’antu masu jarin a kalla yuan miliyan 20, kimanin dalar Amurka miliyan 2.81 ta karu da kaso 2.7 bisa dari a shekara, kamar dai yadda alkaluman da hukumar kididdigar kasar NBS ta fitar a Litinin din nan suka tabbatar.

Sashen masana’antun samar da kayayyakin sarrafawa ne ke kan gaba wajen zaburar da karin ribar masana’antun, sashen da ya samar da karuwar kaso 22.9 bisa dari na ribar, a gabar da fannonin dake bukatar kayayyakin sarrafawar ke kara farfadowa, wanda hakan ya ingiza karuwar farashi. (Saminu Alhassan)