logo

HAUSA

Masana kimiyya sun samu sabuwar taswira da ke nuna sinadaran duniyar wata

2023-11-27 20:33:35 CMG Hausa

Kwanan nan, mujallar ilimi ta kasa da kasa wato Nature Communications ta wallafa wani muhimmin sakamakon bincike da masana kimiyyar kasa da kasa karkashin jagorancin masana kimiyya na kasar Sin a fannin binciken wata. Tawagar ta hada bayanai daga samfurin duniyar wata daga lokuta daban-daban domin samar da sabuwar taswira mai inganci dake nuna sinadarai na duniyar wata. Sakamakon wannan binciken na da matukar muhimmanci wajen gano yadda maganadisu ke aiki a karshen wata.

Tsarin sinadarai na saman wata yana samar da bayanan game da samuwa da yanayin juyin halittar wata, wanda ke da mahimmanci don bayyana abubuwan da ke tattare da sifofin da kuma tarihin ma'adinai na wata. (Yahaya)