logo

HAUSA

Jami’ar MDD: Sin mai ba da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin zamani na duniya

2023-11-27 15:22:55 CMG Hausa

Sakatariyar hukumar dokokin cinikayya ta kasa da kasa ta MDD (UNCITRAL), Anna Joubin-Bret, ta bayyana cewa, kasar Sin ta kasance mai bayar da gagarumar gudummawa wajen inganta bude kofa, hada kai, da nuna adalci ga tsarin tattalin arzikin zamani na duniya.

Jami’ar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cikin wata rubutacciyar hira cewa, cinikayya ta kafar Intanet na taka muhimmiyar rawa, wajen tsara yanayin kasuwancin kasa da kasa, kuma ana hasashen muhimmancinsa zai bunkasa nan gaba.

Joubin-Bret ta kuma fahimci musamman saurin bunkasuwar fasahohin zamani na kasar Sin a fannin ciniki, kamar manyan bayanai, da sauran kafofin sadarwar zamani a sassan masana'antu daban-daban. (Ibrahim)