logo

HAUSA

Sin na aiwatar da matakan dakile yaduwar cututtukan numfashi

2023-11-27 11:12:51 CMG Hausa

Yayin da ake kara shiga hunturu, mahukunta a kasar Sin na ci gaba da aiwatar da matakai na dakile yaduwar cututtukan numfashi dake karuwa a wannan lokaci.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Lahadi, kakakin hukumar kiwon lafiya ta kasar Mi Feng, ya ce cututtukan da ake fama da su a halin yanzu, na bazuwa ne sakamakon yaduwar nau’o’in kwayoyin cututtukan mura.

Mi Feng ya kara da cewa, hukumar kiwon lafiyar kasar ta umarci kananan yankuna da su aiwatar da tsare-tsaren gwaje-gwaje, da jinya da aka tanada, kana su wayar da kan al’umma game da wuraren da aka tanada domin yakar cututtukan yara, da asibitocin yaki da zazzabi, da taimakawa marasa lafiya wajen zuwa asibitoci mafiya kusa da su.

Kasar Sin ta fara aiwatar da tsarin ganin marasa lafiya, da rubuta magani ta yanar gizo, a wani mataki na cin gajiyar hidimomin kiwon lafiya ta yanar gizo da aka kafa, domin shawo kan cututtuka masu nasaba da zazzabi, da na magance cututtukan yara. (Saminu Alhassan)