logo

HAUSA

Sabon layin dogo ya hada Lijiang da Shangri-la a kudu maso yammacin kasar Sin

2023-11-26 15:51:17 CMG Hausa

 

A yau Lahadi ne aka bude layin dogo da ya hada biranen Lijiang da Shangri-la, fitattun wuraren shakatawa a lardin Yunnan na kudu masa yammacin kasar Sin, a cewar hukumomin kasar.

Da fara aikin wannan layin dogo na Lijiang da Shangri-la, tsawon lokacin zirga-zirga mafi sauri tsakanin biranen biyu zai kasance awa 1 da mintuna 18.

Hari la yau, layin dogon mai nisan kilomita 139 ya hada Shangri-la, da ke yankin Diqing mai cin gashin kansa na lardin Yunnan, da Kumming, babban birnin lardin.

Sabon layin dogon zai taimaka wajen inganta harkokin sufuri a yankunan da aka fi samun mabambantan kabilu, wanda zai sa kaimi ga hadin kan kasa, da tabbatar da zaman lafiyar kan iyakoki, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar lardin Yunnan, a cewar babban kamfanin jirgin kasa na kasar Sin. (Yahaya)