logo

HAUSA

Karfin makamashin da ake sabuntawa na kasar Sin ya karu cikin watan Janairu zuwa na Oktoba

2023-11-26 15:45:23 CMG Hausa

Karfin makamashi mai tsaftar da kasar Sin ta samar ya karu a cikin watanni 10 na farkon wannan shekara, a daidai lokacin da kasar ke kara bunkasa koren muhalli.

Ya zuwa karshen watan Oktoba, karfin wutar lantarki mai aiki da hasken rana da aka samar a kasar ya karu zuwa kilowatts miliyan 540, inda karuwar ta kai kashi 47 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, yayin da wanda ake samar wa da karfin iska ya kai kilowatt miliyan 400, wanda ke nuna karuwar kashi 15.6 cikin dari a shekara, kamar yadda bayanai daga hukumar kula da makamashi ta kasar (NEA) suka nuna.

Hukumar ta NEA ta ce, kasar ta kara karfin samar da wutar lantarkinta zuwa kimanin kilowatt biliyan 2.81, wanda ya karu da kashi 12.6 cikin dari idan aka kwtanta da makamancin lokacin a bara.

Kasar Sin ta kara yawan jarin da take zubawa a fannin makamashi mai tsafta a cikin ‘yan shekarun nan, yayin da kasar ke yunkurin rage amfani da makamashi mai aiki da iskar Carbon da kuma bunkasa koren muhalli.

Alkaluman sun nuna cewa, a cikin watanni 10 na farkon shekarar, manyan kamfanonin samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana a kasar sun zuba jarin Yuan biliyan 269.4, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 37.86, wanda ya karu da kashi 71.2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. (Yahaya)