logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Halarci Taron Sin Da Japan Da Korea ta Kudu

2023-11-25 21:01:21 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta sanar a yau cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, zai halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu, a Busan na Korea ta Kudu a gobe Lahadi 26 ga wata. (Fa’iza Mustapha)