logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin zai halarci bikin budewar CISCE

2023-11-24 11:15:03 CMG Hausa

Zhang Shaogang, mataimakin shugaban majalisar raya cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje, ya sanar a yau Juma’a cewa, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci bikin bude bikin baje kolin kasa da kasa na tsare-tsaren samar da kayayyaki (CISCE) karo na farko, kuma dandalin tattaunawar kirkire-kirkire da ci gaban harkoki a fannin tsarin samar da kayayyaki, da ma wasu ayyuka da suka jibanci haka, da za a shirya a ranar 28 ga wata a birnin Beijing na kasar Sin, tare da gabatar da muhimmin jawabi. (Mai fassara: Bilkisu Xin)