logo

HAUSA

Ya zuwa karshen shekarar bara tsayin manyan titunan mota na kasar Sin ya kai kilomita 177,000

2023-11-24 09:54:04 CMG Hausa

Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce ya zuwa karshen shekarar 2022 da ta gabata, tsayin manyan titunan mota na kasar Sin ya kai kilomita 177,000, yayin da kasar ke ci gaba da rike kambin kasa mafi tsayin irin wadannan hanyoyi a duniya baki daya.

Da yake karin haske game da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, jami’i a ma’aikatar Guo Sheng, ya ce matsakaicin zango da mota za ta iya ci a tsayin manyan hanyoyin kasar ya kai kilomita miliyan 5.35, adadin da ya karu da kilomita miliyan 1.12 cikin shekaru 10 da suka gabata.

Jami’in ya kara da cewa a shekarun baya bayan nan, manyan hanyoyin mota na kasar Sin na ci gaba da kyautata ta fuskar tsayi da inganci, inda ake ci gaba da kammala manyan ayyuka masu nasaba da hakan.

Guo ya ce a nan gaba kuma, Sin za ta kara inganta hadakar manyan hanyoyin mota, da kara azamar gina ababen more rayuwa na zamani, domin tabbatar an kyautata sufurin jama’a da kayayyaki. (Saminu Alhassan)