logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Yi Gwajin Bayar Da Damar Shiga Kasar Ba Tare Da Visa Ba Ga Karin Kasashe 6

2023-11-24 18:55:16 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, kasar Sin za ta yi gwajin bayar da izinin shiga kasar ba tare da visa ba ga mutanen kasashen Faransa da Jamus da Italiya da Netherlands da Spaniya da Malaysia, daga ranar 1 ga watan Disamban bana, zuwa 30 ga watan Nuwamban shekarar 2024.

Kakakin ma’aikatar Mao Ning, ta ce za a ba da damar shiga kasar Sin ba tare da Visa ba na tsawon kwanaki 15 ga jama’ar wadannan kasashe masu fasfo da ba na musammam ba, wadanda za su shigo kasar Sin domin kasuwanci ko yawon bude ido ko ziyartar iyalai da abokai, ko domin yada zango.

Mao Ning ta kara da cewa, wannan kokari na da nufin kyautata musaya tsakanin kasar Sin da kasashen ketare domin samun ci gaba mai inganci da kara bude kofar kasar. (Fa’iza Mustapha)