logo

HAUSA

Kasar Sin Na Fatan Taro Kan Sauyin Yanayi Zai Warware Matsalolin Da Kasashe Masu Tasowa Ke Fuskanta

2023-11-24 20:11:57 CMG Hausa

Za a gudanar da taron duniya kan sauyin yanayi a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamba. Kuma domin tunkarar matsalar sauyin yanayi yadda ya kamata da karfafa dadaddiyar huldar abota dake tsakanin Sin da UAE, mataimakin firaministan Sin Ding Xuexiang, zai halarci taron a matsayin wakili na musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ce ta sanar da hakan a yau, inda ta ce kasar Sin za ta nemi dukkan bangarori su yi kokarin daukaka tsare-tsare da ka’idoji da manufofin yarjejeniyar MDD kan sauyin yanayi wato UNFCC, musamman ka’idar daukar nauye-nauye mabambanta dake kan kowa da kuma taken taron na “hada hannu da daukar mataki da samun sakamako”, ta yadda za a warware matsaloli da batutuwan da kasashe masu tasowa ke fuskanta da inganta aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris yadda ya kamata.

Kakakin ta kuma sanar da cewa, bisa gayyatar da mataimaki na 1 na firaministan kasar Kazakhstan Roman Sklyar da mataimakin firaminista kuma ministan harkokin wajen Turkmenistan Rashid Meredov su ka yi masa, mataimakin firaministan na Sin, Ding Xuexiang zai ziyarci kasashen Kazakhstan da Turkmenistan daga ranar 26 zuwa 30 ga watan Nuwamba. (Fa’iza Mustapha)