logo

HAUSA

An gudanar da bikin “Reel Africa” a birnin Shanghai

2023-11-24 11:03:13 CMG Hausa

Daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Nuwamba ne, aka shirya bikin baje kolin fina-finai na Sin da Afirka mai suna “Reel Africa”, a birnin Shanghai na kasar Sin, wanda cibiyar fassarar fina-finai da shirye-shiryen talabijin na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, da ofishin CMG dake Shanghai, suka shirya, inda aka nuna kyawawan fina-finai daga kasashen Afirka da Sin.

A yayin bikin, mutane masu sana’ar daukar fina-finai ta Sin da Afirka sun tattauna kan dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka, da ma hadin gwiwar da suke a fannin fina-finai da shirye-shiryen talabijin.

A wajen wannan biki mai taken "Matan Sin da Afirka a cikin fina-finai", an nuna fina-finai guda shida daga kasashen Najeriya, da Tanzania, da Kenya da Sin, wadanda suka taimakawa Sinawa masu kallo, kara fahimtar hakikanin rayuwar matan Afirka, da kara kusanto da jama’ar Sin da kasashen Afirka.

A jawabinta, shugabar cibiyar fassara fina-finai da shirye-shiryen talabijin ta CMG Wang Lu ta bayyana fatan cewa, bikin "Reel Africa" zai gina wata gadar mu'amalar al'adu tsakanin Sin da Afirka, da shimfida hanyar musaya da koyi da juna kan wayewar kai tsakanin bangarorin biyu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)