logo

HAUSA

Xi ya sha alwashin bunkasa hadin gwiwa da zababben shugaban Liberia

2023-11-23 13:40:57 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da sabon zababben shugaban kasar Liberia Joseph Nyumah Boakai, ta yadda sassan biyu za su zurfafa kawance da amincewa da juna, da karfafa hadin gwiwar cimma moriya tare.

Xi ya bayyana hakan ne a ranar Talata, cikin sakon taya murnar lashe zabe da ya aikewa shugaba Boakai.  (Saminu Alhassan)