logo

HAUSA

Sin ta yi kokari tare da kasa da kasa wajen kafa tsari mai inganci na samar da kayayyaki da sayar da su a duniya

2023-11-23 20:35:09 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kasar Sin ta samu moriya kuma ta tabbatar da tsarin hadin gwiwa na samar da kayayyaki da sayar da su a duniya. Ta ce kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, da yin kokari tare da kasa da kasa wajen kafa tsari mai inganci da amfani na samar da kayayyaki da sayar da su, domin samun moriyar juna a duniya.

Za a gudanar da bikin baje koli na sa kaimi ga samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na farko a birnin Beijing a mako mai zuwa.

Mao Ning ta bayyana cewa, a gun bikin baje kolin, za a kafa sassa biyar da suka hada da na motoci masu fasahar zamani da aikin noma ba tare da gurbata muhalli ba da makamashi mai tsabta da kimiyya da fasahar sadarwa da zaman rayuwa mai inganci, da kuma sashen ba da hidimar samar da kayayyaki.

Ya zuwa yanzu kamfanoni fiye da 500 daga kasashe da yankuna 55 sun tabbatar da za su halarci bikin. Wannan ya shaida cewa, an tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta hanyar tabbatar da samar da kayayyaki da sayar da su, lamarin da ya dace da moriyar kasa da kasa.(Zainab)