logo

HAUSA

Fasahar 5G a kasar Sin ta samu ci gaba mai dorewa

2023-11-23 11:11:18 CMG Hausa

Kasar Sin na samun ci gaba wajen gina hanyar sadarwa ta 5G a kokarin da take yi na ciyar da sauye-sauyen fasahar zamani na hakikanin tattalin arzikinta gaba.

Kasar ta gina kusan tashoshin 5G miliyan 3.22 ya zuwa karshen watan Oktoba, wanda ya kai kashi 28.1 cikin dari na dukkan tashoshin wayoyin salula, a cewar ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar.

Manyan kamfanonin sadarwa guda uku na kasar Sin, China Mobile, China Telecom da China Unicom suna da masu amfani da wayar salula ta 5G da yawansu ya kai miliyan 754 a karshen watan Oktoba.

Har ila yau, alkaluman da ma’aikatar ta fitar sun nuna yadda masana’antar sadarwa ta kasar Sin ta fadada a cikin watanni 10 na farkon shekara. Adadin kudaden shigan kamfanoni a wannan fannin ya kai kusan kudin Sin yuan tiriliyan 1.4 kimanin dalar Amurka biliyan 197.9, wanda ya karu da kashi 6.9 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. (Yahaya)