logo

HAUSA

Sin za ta gaggauta kafa tsarin bibiyar adadin iskar carbon yayin sarrafa hajoji

2023-11-23 10:23:08 CMG Hausa

Kasar Sin za ta gaggauta kafa tsarin bibiyar adadin iskar carbon mai dumama yanayi da ake fitarwa yayin sarrafa hajoji a masana’antun daidaita da yanayin kasar, kana za ta samar da babban rumbun adana bayanai kan hakan, tare da samar da tsarin bayyana matsayin iskar carbon da aka fitar kan kayan da aka sarrafa, da ma tsarin samar da takardun shaidar hakan.

Wannan na kunshe ne cikin wasu ka’idojin aiki da aka fitar a jiya Laraba, bisa hadin gwiwar hukumar samar da ci gaba da gudanar da sauye sauye ta kasar ko NDRC, da wasu hukumomin gwamnati 4.

A cewar hukumar NDRC, ka’idojin za su taimakawa kamfanoni wajen tsimin makamashi, da rage fitar da iskar carbon mai dumama yanayi, da fadada samar da hajoji da ake sarrafawa ta hanyar fitar da mafi karancin iskar carbon, tare da inganta ikon takara na hajojin cinikayyar waje ta kasar.

Tuni dai kasar Sin ta sanar da kaiwa kololuwar fitar da iskar carbon nan zuwa shekarar 2030, da kuma aiwatar da manufofin kawar da tasirin iskar ga yanayi nan da shekarar 2060. (Saminu Alhassan)