logo

HAUSA

Ministar harkokin wajen Faransa za ta ziyarci kasar Sin

2023-11-22 20:13:44 CMG Hausa

 

Bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi mata, ministar kula da harkokin waje da Turai ta kasar Faransa, Catherine Colonna za ta ziyarci kasar Sin daga ranar 23 zuwa 24 ga watan nan na Nuwamba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta sanar da hakan, inda ta ce yayin ziyarar, za a yi taro karo na 6 tsakanin Sin da Faransa kan musaya tsakanin al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha)