logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gana da shugaban majalisar wakilai ta Duma ta Rasha

2023-11-22 16:53:24 CMG Hausa

A yau 22 ga wannan wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar wakilai ta Duma ta kasar Rasha Vyacheslav Viktorovich Volodin a babban dakin taron jama’a dake nan birnin Beijing na kasar Sin. 

A yayin ganawar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana son hada hannu da kasar Rasha wajen sada zumunta da hadin gwiwa da raya dangantakar samun moriyar juna a tsakanin kasashen biyu, don samar da kuzari ga farfado da bunkasuwar kasashen biyu da tabbatar da samun wadata da zaman lafiya a duniya baki daya. Ya kuma yi fatan majalisar wakilai ta Duma ta kasar Rasha za ta kara yin mu’amala da majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a fannin tsara dokoki, don samar da goyon baya ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin dokoki, da tabbatar da raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya da kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya, da zurfafa hadin gwiwa bisa tsarin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kungiyar BRICS, da kungiyar G20 da sauransu.

A nasa bangare, Volodin ya bayyana cewa, kasar Rasha tana son kara hadin gwiwa da hukumomin tsara dokoki na Sin da jam’iyyun Sin, da aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito kansu, da sada zumunta da kara yin imani da juna a tsakanin jama’ar kasashen biyu, don tabbatar da raya dangantakar abokantaka mai dorewa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Rasha da Sin, da samar da gudummawa wajen samun bunkasuwa a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)