logo

HAUSA

An yi shawarwari na farko tsakanin ministocin wajen Sin da Uzbekistan

2023-11-22 09:24:14 CMG Hausa

A jiya ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi shawarwari na farko bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Uzbekistan tare da takwaransa na Uzbekistan Bakhtiyor Saidov.

Bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi da samun cikakkiyar fahimta, tare da cimma matsaya, kan yadda za a aiwatar da muhimman ra'ayoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa hadin gwiwar dabarun samun ci gaba, da ma sanar da tsara wata hanyar tattaunawa tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu. (Ibrahim)