logo

HAUSA

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Wucin Gadi Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila

2023-11-22 20:09:16 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi da aka cimma tsakanin bangarorin Palasdinu da Isra’ila, kuma tana fatan yarjejeniyar za ta taimaka wajen saukaka matsalolin jin kai da rage tsanantar rikicin da ma zaman dardar a yankin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta bayyana hakan, yayin taron manema labarai na yau Laraba. (Fa'iza)