logo

HAUSA

Sin da Uruguay na sanya ido kan sabbin damarmakin hadin gwiwa

2023-11-22 09:30:40 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, a yayin ziyarar da shugaban kasar Uruguay Luis Alberto Lacalle Pou ya kawo kasar Sin, wakilan ‘yan kasuwar kasashen biyu fiye da 260 ne, suka halarci taron tattaunawa kan yadda za a raya hadin gwiwar cinikayya tsakanin kasashen biyu jiya Talata, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan sabbin damarmakin hadin gwiwa.

Shugaban kasar Uruguay Luis Alberto Lacalle Pou ya bayyana a yayin taron cewa, yana fatan bangarorin biyu, za su cimma matsaya na dogon lokaci, da kara karfafa hadin gwiwa a aikace a fannoni daban daban, da ba da gagarumar gudummawa, wajen raya alakar dake tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci. (Ibrahim)