logo

HAUSA

Kasar Sin Na Gayyatar ‘Yan Kasuwa Daga Fadin Duniya Don Su Zuba Jari Da Ma Cin Gajiyar Nasarorin Da Ta Samu

2023-11-21 20:14:37 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce juriya da damarmaki da kuzarin da tattalin arzikin kasar Sin ke da su da kuma manufar kasar ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, baya ga babbar kasuwa da kasar ta mallaka, su ne dalilan da suka sa ‘yan kasuwa daga sassan duniya ke son zuwa kasar.

Mao Ning ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Talata, inda ta nanata cewa, yayin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sake jaddada cewa, kasarsa za ta inganta dabarunta na kare hakkoki da muradun masu zuba jari na kasashen waje da kara rage jerin bangarorin kasuwanci da aka haramta musu zubawa jari da tabbatar da ana ba masu zuba jari kulawa kamar yadda ake ba ‘yan kasa.

A cewarta, wannan sako ne mai karfi da Sin take aikewa cewa, za ta ci gaba da fadada bude kofarta. Haka kuma gayyata ce ga ‘yan kasuwa daga sassan duniya su zo su zuba jari a kasar tare da cin gajiyar nasarorinta. (Fa’iza Msutapha)