logo

HAUSA

Xi: Ya Zama Wajibi Kasashen BRICS Su Yi Kira Da A Tabbatar Da Adalci Da Zaman Lafiya Dangane Da Batun Palasdinu Da Isra’ila

2023-11-21 22:29:11 CMG Hausa

Da yammacin yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taro na musamman na shugabannin kungiyar BRICS kan batun Palasdinu da Isra’ila.

Xi Jinping wanda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing, ya bayyana cewa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki, ya zama wajibi kasashen BRICS su nemi a tabbatar da adalci da zaman lafiya kan batun Palasdinu da Isra’ila.

A cewarsa, abu mafi dacewa da kawo karshen rikicin da yaki-ci-yaki-cinyewa tsakanin Palasdinu da Isra’ila shi ne kafa kasashe biyu da mayar da halaltattun hakkokin Palasdinu da kafa ‘yantacciyar kasar Palasdinu.

Ya ce, idan har ba a warware matsalar bisa adalci ba, to, ba za a taba samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya ba.

Ya kuma gabatar da shawarwari 3 game da warware batun, yana mai kira da a dakatar da bude wuta domin cimma zaman lafiya da tsaro mai dorewa. Kuma dukkan bangarori masu rikici su dakatar da bude wuta da dukkan wani nau’i na rikici da kai hari kan fararen hula. Haka kuma a saki fararen hular da ake tsare da su domin kaucewa karuwar asarar rayuka da wahalhalu. Ya ce, wajibi ne a tabbatar da wucewar kayayyakin agaji ba tare da tangarda ba da fadada ayyukan agajin jin kai ga mutanen Gaza da dakatar da tilasta musu kaura da yanke wuta da ruwa da mai da ake wa al’ummar Gaza a matsayin hukunci na gama gari.

Bugu da kari, shugaban na Sin ya yi kira ga kasa da kasa da su dauki kwararan matakai domin kaucewa tsanantar rikicin da bazuwar tasirinsa kan baki dayan yankin Gabas ta Tsakiya. (Fa’iza Mustapha)