logo

HAUSA

Mataimakin firaministan Sin ya jaddada bukatar raya masana’antun samar da fasahar intanet mai karfin 5G

2023-11-21 09:37:07 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing ya yi kira da a yi kokarin gaggauta bunkasa masana’antun samar da fasahar intanet ta 5G.

Zhang ya bayyana haka ne a yayin bikin bude taron masana’antun yanar gizo na 5G+ na kasar Sin da aka gudanar a birnin Wuhan na lardin Hubei dake yankin tsakiyar kasar

Ya ce, manufar wannan kokari ita ce, inganta sabbin masana’antu da gina tsarin masana’antun kasar na zamani.

Mataimakin firaministan ya ce, yayin da ake ci gaba da zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki na zamani da sashen samar da kayayyaki da na hidima, ya kamata kasar ta hanzarta yiwa masana'antun garambawul, da inganta su da fasahohin zamani, da intanet da fasahohin kwaikwayon tunanin dan-Adam.

Ya ce, ya kamata a zage damtse don inganta kayayyakin intanet, da hanzarta amfani da fasahohin intanet da ma karfafa tsaron fasahar. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)