logo

HAUSA

Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa

2023-11-20 20:08:46 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a yau Litinin.

Yayin tattaunawar, shugaban Sin Xi Jinping ya ce, a shekarar 2024 kasashen biyu za su cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya. Kuma kasar Sin ta shirya ci gaba da musaya da Faransa domin samun nasarar shirya taron koli na musaya tsakanin al’ummun kasashen biyu da ingiza sabuwar nasara a hadin gwiwarsu a fannonin raya al’adu da ilimi da binciken kimiyya da daukaka musayar abota tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

A nasa bangare, Emmanuel Macron ya bayyana cewa, bisa la’akari da yanayin da duniya ke ciki, ci gaba da tuntubar juna da hadin gwiwa tsakanin Faransa da Sin, abu ne mai muhimmanci ga kasarsa. Kuma a shirye Faransar take ta matsa kaimi wajen musaya da Sin da zurfafa musayar da hadin gwiwa a bangarorin tattalin arziki da cinikayya da sufurin sama da ma tsakanin al’ummominsu.

Har ila yau, shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayi kan rikicin Palasdinu da Isra’ila. Kuma sun yi imanin cewa, wajibi ne a kaucewa kara tabarbarewar yanayin, musammam samun matsalar jin kai mai tsanani. Haka kuma, kafa kasashe biyu masu ‘yancin kansu, ita ce hanyar warware rikicin Palasdinu da Isra’ila da taki-ci-taki-cinyewa. (Fa’iza Mustapha)