logo

HAUSA

Adadin cinikin na’urorin sabbin fasahohi a baje koli karo na 25 ya kai yuan biliyan 37.2

2023-11-20 10:06:36 CMG Hausa

Rahotannin game da bikin baje kolin na’urorin sabbin fasahohin zamani na kasa da kasa na kasar Sin karo na 25 da aka kammala a jiya Lahadi a birnin Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, sun nuna cewa, jimillar ‘yan kallon da suka shiga bikin ta kai dubu 248, kuma darajar cinikayyar da aka yi yayin bikin ta kai kudin Sin yuan biliyan 37.279.

Babban taken bikin shi ne “Bunkasa kuzarin kirkire-kirkire domin kyautata ingancin ci gaba”, wanda ya samu halartar kamfanoni sama da 4000 da suka zo daga kasashe da yankuna 105. Yayin bikin, an gudanar da manyan ayyuku har 132, inda aka gabatar da sabbin na’urori 681.

Abun faranta rai shi ne, a karon farko an shirya nune-nunen fasaha da kimiyyar binciken sararin samaniya, inda kamfanonin da abin ya shafa fiye da 200 suka baje kolin na’urorin zamani iri daban daban, wadanda suka hada da na’urorin zirga-zirgar sararin samaniya, da rokoki, da taurarin dan Adam, da na’urorin binciken sararin samaniya da sauransu. (Jamila)