logo

HAUSA

Masana na kasa da kasa na taro game da amfani da fasahohin sararin samaniya ta hanyoyin lumana

2023-11-20 11:29:19 CMG Hausa

An bude taron kasa da kasa game da amfani da fasahohin sararin samaniya ta hanyoyin lumana na shekarar 2023, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Taron na yini 3, wanda aka bude a ranar Asabar, ya hallara masana kimiyya, da kwararru sama da 100 daga ciki da wajen kasar Sin, wadanda suka maida hankali ga tattauna batutuwan da suka jibanci yadda za a bunkasa, da cimma gajiya daga fasahohin sararin samaniya ta hanyoyin lumana, da yadda za a yayata musaya, da hadin gwiwar sassan kasa da kasa a wannan fanni.

Har ila yau, taron ya ba da damar musayar ra’ayoyi game da muhimman batutuwa da suka kunshi yanayin makamashi a samaniya da a doron duniya, da zuba jari a masana’antun binciken samaniya, da raba ilimin kimiyya da fasahohin binciken samaniya, da raya hada-hadar cinikayya mai nasaba da hakan, da bunkasa ci gaba da hadin gwiwa a fannin.

Da yake tsokaci yayin taron, babban darakta a kungiyar gamayyar masana binciken sararin samaniya ta kasa da kasa Christian Feichtinger, ya ce Sin ta yi rawar gani wajen ba da gudummawar raya fasahohin binciken samaniya, ta kuma cimma manyan nasarori.

Feichtinger ya kara da cewa, yayin taron na wannan karo, yana fatan masana da kwararru mahalartansa za su cimma matsaya game da amfani da fasahohin sararin samaniya ta hanyoyin lumana, da tabbatar da ganin fasahohin da ake samu sun amfani karin al’ummu a nan gaba. (Saminu Alhassan)