logo

HAUSA

Hadaddiyar Tawagar Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Za Ta Ziyarci Kasar Sin

2023-11-19 20:45:50 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, wata hadaddiyar tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na musulmi za ta ziyarci kasar Sin daga ranar 20 zuwa 21 ga wata.

Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka a yau Lahadi, inda ta ce, tawagar ta hada da ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud da mataimakin firaministan Jordan, kuma ministan harkokin wajen kasar Ayman Safadi da takwaransa na Masar Sameh Shoukry da kuma ministar harkokin wajen kasar Indonesia madam Retno Marsudi. Sauran sun hada da ministan harkokin wajen Palasdinu Riyad al-Maliki da sakatare janar na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa (OIC) Hussein Ibrahim Taha.

Yayin ziyarar, bangaren Sin zai yi tattaunawa mai zurfi tare da hada hannu da tawagar ministocin harkokin waje na kasashen na Larabawa da na musulmi, wajen ganin an yayyafawa rikicin Palasdinu da Isra’ila cikin ruwan sanyi tare da kare fararen hula da warware matsalar ta hanyar da ta dace. (Fa’iza Mustapha)