logo

HAUSA

Bangarori daban daban sun yabawa jawabin Xi Jinping a yayin kwarya-kwaryan taron APEC

2023-11-19 16:37:24 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasifik ko APEC karo na 30, wanda ya ja hankalin kasa da kasa sosai. Wasu mutane daga kasashe da dama sun bayyana cewa, shugaba Xi ya yi nazari kan yanayin bunkasuwar yankin a wannan lokaci, da kiyaye hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik don nuna taswirar raya yankin a shekaru 30 masu zuwa. Sun kuma yi imanin cewa, kasar Sin za ta sa kaimi ga samun karin nasarori kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Asiya da tekun Pasifik, da samar da sabbin gudummawa wajen samun ci gaba a yankin har ma a duk duniya baki daya.

Direkten sashen nazarin ilmin siyasa na jami’ar Cape Town ta kasar Afirka ta Kudu Mbulle-Nziege Leonard ya bayyana cewa, kasar Sin tana da fasahohi masu tarin yawa wajen yaki da talauci. Ya ce cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin ta cimma burin fitar da mutane mafi yawa daga kangin talauci, kuma idan aka yi la’akari da bunkasuwar yankin, fasahohin Sin ba ma taimakawa mata samun ci gaba ba kadai za su yi ba, har ma da taimakawa sauran kasashen Asiya da tekun Pasifik.  

A nasa bangare, masanin harkokin tattalin arziki da siyasa na kasar Ruwanda, Rusa Bagirishya ya bayyana cewa, Sin ta samu manyan nasarori na ci gaba, har ma ta samar da gudummawa wajen zamanintar da kasa da kasa a duniya, lamarin da ya kawo kyakkyawan fata ga kasashe masu neman samun bunkasuwa cikin lumana. (Zainab)