logo

HAUSA

Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-7 Na Kasar Sin Ya Isa Tashar Harba Kumbuna Ta Kasar

2023-11-19 16:04:18 CMG Hausa

Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin, ta bayyana a yau Lahadi cewa, kumbon dakon kaya na Tianzhou-7, ya isa cibiyar harba kumbuna ta kasar.

A cewar hukumar, za a harhada kumbun tare da aiwatar da gwaje-gwaje da sauran wasu ayyuka, kafin daga bisani a harba shi daga tashar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin a farkon badi.

Har ila yau, hukumar ta fitar da tamburan ayyukan harba kumbuna 4 da za a yi a shekarar 2024 da suka hada da kumbunan dakon kaya na Tianzhou-7 da Tianzhou-8 da kumbunan Shenzhou-18 da Shenzhou-19 da za su dauki ‘yan sama jannati.

Tun bayan kammala gininsa a shekarar 2022, tashar sararin samaniya ta Sin ta shiga matakin sanya kayayyaki da tsara fasali, wanda zai dauki shekaru sama da 10, inda a ko wace shekara, za a harba kambuna 2 dauke da ‘yan sama jannati da wasu kumbon dakon kaya daya ko biyu. (Fa’iza Mustapha)