logo

HAUSA

CGTN ya gabatar da shiri kan ganawar shugabannin Sin da Amurka

2023-11-18 10:09:31 CMG Hausa

A ranar 15 ga wata, bisa agogon wurin, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, a birnin San Francisco na kasar Amurka, inda suka yi musayar ra'ayi kan wasu manyan batutuwan da suka shafi huldar dake tsakanin kasashen 2, gami da yunkurin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a duniya. Don bayyana yanayin da huldar kasashen biyu ke ciki, da hanyar da ya kamata su bi don inganta hulda da juna a nan gaba, gidan telabijin na CGTN ya gabatar da wani shirin bidiyo na musamman mai taken "Ketare tekun Pasific, da tantance huldar dake tsakanin Sin da Amurka".

A cikin shirin, an nuna cewa, mutunta juna a tsakanin mutane ko kasashe shi ne tushen abokantaka. Kasar Sin na hulda da sauran kasashe ne, ta bisa manufar mutunta juna. Sahihancin da kasar ta nuna a fannonin cudanyar gwamnatoci da al'ummu, ya taimaka wajen daidaita ra'ayi na kuskure da bahaguwar fahimta da ake samu tsakanin manyan kasashe. Sa'an nan, a wannan zamanin da muke ciki da ake fuskantar tashin hankali da rikici irin daban daban a duniya, ya kamata kasashen Sin da Amurka su hada gwiwa wajen sauke nauyin dake bisa wuyansu a matsayinsu na manyan kasashe, don bayar da gudunmowa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya, da ci gaba na bai daya a duk fadin duniya. (Bello Wang)