logo

HAUSA

Wang Yi ya yi fashin baki game da ziyarar shugaba Xi a Amurka

2023-11-18 22:02:47 CMG

Bisa gayyatar da takwaransa na Amurka Joe Biden ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyara birnin San Francisco, inda ya halarci taron shugabannin Sin da Amurka, da kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC karo na 30 a birnin na San Francisco. Shugaba Xi ya gudanar da wannan ziyara ne tsakanin ranaikun 14 zuwa 17 ga watan Nuwamban nan.

A karshen wannan ziyara, mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya yi wa manema labarai fashin baki game da ziyarar. Wang ya ce a halin da ake ciki, duniya na fama da manyan sauye sauye, kuma al’ummun duniya na fuskantar sabon yanayi a tarihi. Ya ce alkiblar alakar Sin da Amurka na da matukar tasiri ga al’ummun kasashen biyu, da ma al’ummun duniya baki daya.

Kaza lika, a bana ake ciki shekaru 30 tun bayan kiran taron shugabannin APEC na farko, kuma dukkanin sassa na mayar da hankali ga makomar hadin gwiwar yankin Asiya da Fasifik a shekaru 30 masu zuwa. A wannan gaba mai muhimmanci, shugaba Xi Jinping ya ratsa tekun Fasifik, inda ya gudanar da ziyarar aiki a San Francisco. Har ila yau ya gana da shugaba Biden, da nufin zakulo turba ta gari ta kyautata zaman jituwa tsakanin Sin da Amurka; tare da yin cudanya da musaya da sassa daban daban na Amurka, da cimma matsayar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu; ya kuma halarci kwarya kwaryar taron shugabannin APEC, tare da nuna alkiblar hadin gwiwar yankin Asiya da Fasifik.

Ra’ayoyin al’ummun kasa da kasa mafi akasari ya karkata ga cewa, ziyarar ta shugaba Xi ta janyo hankalin duniya, ta kuma haifar da manyan nasarori, kuma tana da tarin tasiri, kaza lika za ta ingiza daidaiton alakar Sin da Amurka, da kawo sabon kuzari ga hadin gwiwar yankin Asiya da Fasifik, da ingiza kuzari ga cudanyar sassan kasa da kasa da shiyyoyin duniya.  (Saminu Alhassan)