logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi yayin kwarya-kwaryan taron shugabannin APEC

2023-11-18 04:23:28 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi yayin kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik ko APEC, wanda ya gudana a birnin San Francisco na kasar Amurka a ranar Juma’a bisa agogon wurin.

Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata mu kara inganta hadin-gwiwa tsakanin yankunan Asiya da tekun Pasifik, da amsa kiran zamanin da muke ciki, da shawo kan kalubalen duniya, da aiwatar da ajandar Putrajaya ta kungiyar APEC nan da shekara ta 2040, a wani kokari na raya gamayyar yankunan Asiya da tekun Pasifik mai kuzari da karfi da zaman lafiya, da samar da ci gaba ga al’ummomin yankunan gami da zuriyoyinsu dake tafe.