logo

HAUSA

Xi Jinping ya dawo birnin Beijing daga kasar Amurka

2023-11-18 19:58:50 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya dawo nan birnin Beijing, bayan da ya gudanar da shawarwari tare da takwaransa na Amurka, Joe Biden, tare da halartar kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC karo na 30 a birnin San Francisco.

Da maraicen ranar 17 ga watan Nuwamban nan bisa agogon wurin, mai rikon mukamin magajin garin San Francisco Madam London Breed, da sauran wasu wakilan Amurka, sun yi ban kwana da shugaba Xi a filin tashi da saukar jiragen sama. Kuma a kan hanyarsa zuwa filin saukar jiragen saman, Sinawa dake zaune a Amurka, gami da wakilan daliban kasar dake karatu a wurin, sun rike tutocin kasashen biyu, don ban kwana da shugaba Xi, tare kuma da taya shi murnar kammala ziyara a Amurka cikin nasara. (Murtala Zhang)