logo

HAUSA

Shugaba Xi ya yi kira ga mambobin APEC da su nacewa kirkire-kirkire da aiwatar da matakai a bude yayin bunkasa yankinsu

2023-11-18 05:46:01 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga shugabannin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik ko APEC, da su nacewa kirkire-kirkire, da aiwatar da matakai a bude, da ingiza ci gaba maras gurbata yanayi, kana su rungumi tafiya tare da dukkanin sassa, da cimma moriya tare yayin bunkasa yankinsu.

Xi ya yi kiran ne cikin jawabin da ya gabatar yayin kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC, wanda ya gudana a birnin San Francisco na kasar Amurka a ranar Juma’a bisa agogon wurin.

Har ila yau, shugaban na Sin ya ce kasar sa za ta nacewa manufar samun ci gaba cikin lumana, kasancewar ginshikin samun bunkasuwa shi ne samarwa al’ummun Sin kyakkyawar rayuwa, ba wai maye gurbin wani ba. Ya ce a bana ake cika shekaru 45 da fara aiwatar da manufar Sin ta gudanar da gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.

Bugu da kari, shugaba Xi ya ce "Za mu ci gaba da kokarin samun ci gaba mai nagarta da bude kofarmu. Zamanantarwa ta Sin za ta iya taimakawa wajen zamanantar da duniya a wannan sabon zamani da kuma ciki".

Daga nan sai ya yi kira da a hada karfi da karfe wajen ingiza hadin gwiwa tsakanin sassan yankin Asiya da Fasifik, domin cimma karin nasarori, da gina wasu shekarun nasarori bisa hadin gwiwar yankin cikin shekaru 30 masu zuwa.  (Saminu Alhassan)