logo

HAUSA

Tawagar Sin ta halarci taron ministocin tsaro na ASEAN Plus

2023-11-17 09:42:03 CMG Hausa

Jiya Alhamis ne, tawagar ma'aikatar tsaron kasar Sin, ta halarci taron ministocin tsaron kasashen kungiyar ASEAN Plus (ADMM-PLUS) karo na 10 a birnin Jakarta na kasar Indonesia.

Mai magana da yawun ma'aikatar Zhang Xiaogang ya bayyana cewa, yayin taron, tawagar ta Sin ta yi kira ga dukkan bangarorin, da su aiwatar da tsarin hadin gwiwa na hakika, da kiyaye ingantattun ra'ayoyin tsaro, da yin shawarwari da hadin gwiwa, maimakon sabani da yin fito na fito.

Ban da wannan kuma, tawagar kasar Sin ta bayyana goyon bayan kasar na kasancewar ASEAN a matsayin jigon tsare-tsaren shiyyar, da kuma kudurinta na yin aiki tare da dukkan kasashe mambobin ADMM-PLUS, don samun ci gaba tare, da ba da gagarumar gudummawa, wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Ibrahim)