logo

HAUSA

Shugaba Xi ya gana da shugabannin kasashen Mexico da Peru da firaministan Fiji

2023-11-17 03:40:34 CMG Hausa

Da safiyar Alhamis 16 ga watan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Mexico Andres Manuel Lopez Obrador, a birnin San Francisco na kasar Amurka.

Kaza lika a dai ranar ta Alhamis bisa agogon birnin, shugaba Xi ya gana da shugabar kasar Peru Dina Boluarte, da kuma Firaministan kasar Fiji Sitiveni Rabuka.   (Saminu Alhassan)