logo

HAUSA

An kafa sabbin kamfanoni masu jarin waje 41,947 a kasar Sin cikin watanni 10 na farkon bana

2023-11-17 21:20:32 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ta ce jimilar sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a kasar cikin watanni 10 na farkon bana ta kai 41,947.

A cewarta, adadin ya nuna an samu karuwa da kaso 32.1 a kan na makamancin lokacin a bara, wato shekara 1 da ta gabata. (Fa’iza Mustpha)