logo

HAUSA

Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron tsaro na kungiyar SCO

2023-11-17 20:14:23 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da tsaro ta kasar Sin ta ce za ta karbi bakuncin taron tsaro karo na 5 na kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), daga ranar 20 zuwa 29 ga wata.

Taron zai karbi bakuncin jami’an tsaro da masana da malamai daga kasashe mambobin kungiyar SCO, da kasashe ’yan kallo da kasashe abokan hulda.

Taron wanda zai mayar da hankali kan shawarwari 3 na ci gaban duniya da Sin ta gabatar da tsaron yanki da hadin gwiwa, zai kunshi lakcoci da tattaunawa da ziyarce-ziyarce.

A cewar ma’aikatar tsaron kasar Sin, manufar taron ita ce, karfafa fahimtar juna da aminci tsakanin rundunonin sojin kasashen da hada hannu wajen tattaunawa da lalubo hanyoyi da dabarun zurfafa hadin gwiwar tsaro karkashin tsarin kungiyar da bayar da gudunmawa wajen gina al’ummar SCO mai makoma ta bai daya. (Fa’iza Mustapha)