logo

HAUSA

Sin da Afirka na da makoma mai kyau a fannin hadin gwiwar aikin gona

2023-11-16 10:17:22 CMG Hausa

Jami’ai sun bayyana a gun taron dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin aikin gona karo na biyu cewa, hadin gwiwar a fannin aikin gona tsakanin Sin da Afirka ya haifar da sakamako mai kyau tare da makoma mai haske.

Yayin da yake nuni da cewa hadin gwiwa a fannin aikin gona wata damar samun nasara tare ce ga kasar Sin da Afirka, kwamishinan aikin gona, da raya karkara da tattalin arzikin teku da muhalli mai dorewa na kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Josefa Leonel Correia Sacko, ya bayyana cewa, “Sakamakon da kasar Sin ta samu a kan zamanantar da aikin gona ta hanyar zuba jari mai yawa a fannin binciken kimiyya da fasaha, ya baiwa kungiyar ta AU babbar damar cin gajiya da kuma ciyar da nahiyar Afirka gaba ta fuskar noma, da masana’antun noma da sauye-sauyen tsarin cinikayyar amfanin gona.”

Ana sa ran yawan cinikin amfanin gona tsakanin Sin da Afirka zai zarce dala biliyan 10, a shekarar 2023, wanda ya kusan ninka na shekaru goma da suka gabata, kuma ana sa ran nan da shekaru 10 masu zuwa zai zarce dala biliyan 20. (Yahaya)