logo

HAUSA

Xi ya bukaci a yi dukkan mai yiwuwa yayin gudanar da aikin ceto a gobarar da ta tashi a wani ginin kamfanin hakar kwal

2023-11-16 19:39:23 CMG Hausa

A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da umarnin yin dukkan mai yiwuwa wajen ceto wadanda suka ji rauni a gobarar da ta tashi a wani ginin kamfanin hakar kwal dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin.

Xi Jinping wanda shi ne sakatare-janar na kwamitin kolin JKS, kana shugaban rundunar sojan kasar, ya nemi hukumomi su yi bincike tare da kawar da dukkan barazanar dake akwai a masana’antu, domin kare rayuka da kadarori da ma tsarin rayuwar jama’a. (Faiza Mustapha)