logo

HAUSA

Jarin kai tsaye na kasar Sin a ketare, wanda ba na kudi ba ya karu da kaso 17.3 cikin watanni 10 na farkon bana

2023-11-16 21:36:16 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce jarin kai tsaye na kasar Sin a ketare, wanda ba na kudi ba, ya karu da kaso 17.3 zuwa yuan biliyan 736.2, cikin watanni 10 na farkon bana.

Idan aka kwatanta da dalar Amurka, jarin wanda ba na kudi ba, ya kai dala biliyan 104.74 a wannan lokaci, karuwar kaso 11 daga shekara guda da ta gabata.

A cewar ma’aikatar, daga watan Janairu zuwa Oktoba, jarin a kasashen dake cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, ya kai yuan biliyan 181.69, karuwar kaso 27 a kowacce shekara. (Fa’iza Mustapha)