logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin yana kan tsari mai inganci a Oktoba

2023-11-15 12:19:34 CMG Hausa

A safiyar yau ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya shirya taron manema labarai, inda mai magana da yawun hukumar kididdiga ta kasar Sin Liu Aihua ta bayyana yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki a watan Oktoban shekarar 2023.

A cikin watan na Oktoba, karfin masana’antun kasar na samar da kayayyaki ya zarce yadda ake zato, inda ya karu da kashi 4.6 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara. Ma’aunin masana’antun samar da hidima na kasa, shi ma ya karu da kashi 7.7 bisa 100 a kowace shekara. Darajar jimillar kudaden kayayyakin masarufi da aka sayar, ta kai yuan biliyan 4333.3, wadda ta karu da kashi 7.6 cikin 100 kan na shekarar bara.

Haka kuma darajar kudade da aka samu a bangaren shigowa da fitar da kayayyaki, ta kai yuan biliyan 3541.7, wadda ta karu da kashi 0.9 cikin 100 kan na bara. Daga cikinsu, darajar kudaden da aka samu a bangaren kayayyakin da aka fitar zuwa kasashen waje, ta kai yuan biliyan 1973.6, raguwar kashi 3.1 cikin 100. Yayin da aka samu yuan biliyan 1568.1 daga shigo da kayayyaki, wadda ta karu da kashi 6.4 ciki 100. Alkaluman kayayyakin bukatu (CPI) ya ragu da kashi 0.2 bisa 100 kan na shekarar bara da kuma kashi 0.1 bisa 100 kan na watan da ya gabata.

Baki daya, a cikin watan Oktoba, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da farfadowa da ma bunkasa, tare da manyan alamu dake nuna yadda yake ci gaba da kuma inganta, baki daya, ana iya cewa, tattalin arzikin yana kan tsari mai inganci. (Ibrahim)