logo

HAUSA

Sin ta jaddada bukatar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinu

2023-11-15 18:44:56 CMG Hausa

Mao Ning, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta furta a wajen taron manema labaru da ya gudana a yau Laraba cewa, dangane da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin bangarorin Isra'ila da Falasdinu, kasar Sin ta bayyana ra'ayinta sau da dama, inda ta yi Allah wadai da duk wani matakin dake lahanta fararen hula, da wanda ya keta dokokin kasa da kasa. A cewarta, kasar Sin ta yi kira sau da dama da a gaggauta tsagaita bude wuta, don magance bala'in jin kai mafi tsanani, kana kasar na ta kokarin tuntubar mabambantan bangarori don neman ganin an tabbatar da hakan. Jami'ar ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokari tare da masu ruwa da tsaki don samar da gudunmawa ga yunkurin tsagaita bude wuta, da saukaka matsalar jin kai, gami da wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarorin Isra'ila da Falasdinu ta hanyar zartas da shirin "kasancewar kasashe 2". (Bello Wang)