logo

HAUSA

Sinawa masana kimiyya sama da 1,200 ne suka shiga cikin jerin masu bincike da aka fi amfani da ayyukansu a duniya

2023-11-15 22:18:41 CMG Hausa

Sinawa masana kimiyya sama da 1,200 ne suka shiga cikin sabon jerin masu bincike da aka fi amfani da ayyukansu a duniya, wanda cibiyar nazarin bayanan kimiyya ta duniya wato Clarivate ta fitar. 

Mujallar kimiyya ta kasar Sin China Science Daily ta ruwaito cewa, cibiyar Clarivate ta fitar da jerin sunayen masu bincike da aka fi amfani da ayyukansu na 2023 a yau Laraba, inda jimilar masana kimiyya 6,849 daga sama da cibiyoyi 1,330 a kasashe da yankuna 67 suka shiga jerin, kuma kaso 83.8 sun fito ne daga kasashe da yankuna 10.

Jimilar Sinawa masana kimiyya 1,275 ne aka zaba domin shiga jerin, inda kasar Sin ta zo na biyu a jerin kasashen duniya. A bara Sinawa masana kimiyya 1,169 aka zaba. (Fa’iza Mustapha)