logo

HAUSA

Masanan kimiyya na kasar Sin za su bunkasa noman rogo a Afrika

2023-11-15 17:44:03 CMG Hausa

Masana kimiyyar aikin gona na kasar Sin, sun bayyana shirinsu na bunkasa noman rogo ta hanyar amfani da sabbin nau’ikan rogo masu inganci a nahiyar Afrika da rogon ke zaman abinci mai muhimmanci.

Cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin CATAS, ta bayyana cikin wani shiri cewa, ta tsara amfani da wasu sabbin nau’ikan rogo da ingantattun fasahohin noma a sama da kadada 500,000 na gonakin kasashen Afrika.

Ana sa ran ingantattun nau’ikan da fasahohin za su kara yawan yabanyar da ake samu na rogo da sama da ton 17 a kowacce kadada.

An sanar da shirin ne yayin taro karo na 2 kan hadin gwiwar Sin da Afrika a bangaren aikin gona, wanda aka kammala yau Laraba, a birnin Sanya dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)