logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin zai isa birnin San Francisco na kasar Amurka

2023-11-15 04:49:00 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai isa birnin San Francisco na kasar Amurka a ranar Talata bisa agogon wurin.

Daga ranar 14 zuwa ranar 17 ga wata, Shugaba Xi zai halarci taron shugabannin kasashen Sin da Amurka, da kuma taron karo na 30 na shugabannin mambobin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin yankin Asiya da na tekun Pasific (APEC), bisa gayyatar da takwaransa na Amurka Joe Biden ya yi masa.(Kande Gao)