logo

HAUSA

Shugaba Xi ya isa birnin San Francisco don ganawa da takwaransa na Amurka da kuma halartar taron shugabannin mambobin kungiyar APEC

2023-11-15 08:26:18 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin San Francisco na kasar Amurka a yammacin Talata 14 ga wata bisa agogon wurin, inda zai halarci taron shugabannin kasashen Sin da Amurka bisa gayyatar da takwaransa na Amurka Joe Biden ya yi masa, kana zai halarci kwarya-kwaryan taron shugabannin mambobin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin yankin Asiya da na tekun Pasific (APEC) karo na 30.

Yayin da Shugaba Xi ya isa filin jiragen saman kasa da kasa na San Francisco, ya samu tarba sosai daga wajen gwamnan jihar California Gavin Newsom, sakatariyar baitul-malin Amurka Janet L. Yellen da sauran manyan jami’an Amurka.

Haka zakila, dimbin Sinawan da ke zaune a birnin da wakilan daliban kasar Sin da ke karatu a wurin sun tsaya a gefunan titin da ayarin motocin Shugaba Xi zai wuce, sun daga tutocin Sin da Amurka don yi masa maraba da zuwa. (Kande Gao)