logo

HAUSA

Ana gudanar da dandalin FOCAC game da raya noma

2023-11-14 22:58:51 CMG

Yanzu haka ana gudanar da dandalin hadin gwiwa na Sin da kasashen Afirka ko FOCAC, a fannin raya ayyukan noma a birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. Dandalin na wannan karo, wanda shi ne irin sa na biyu, a wannan lokaci zai gudana ne tsakanin ranaikun 13 zuwa 15 ga watan nan na Nuwamba. Za kuma a yi amfani da shi wajen tattauna yadda za a taimakawa kasashen Afirka, da dabarun zamanantar da noma, ta yadda kasashen nahiyar za su cimma ci gaba mai dorewa a fannin.

Da yake tsokaci yayin taron, ministan noma na kasar Sin Tang Renjian, ya ce tun bayan gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya ko BRI shekaru 10 da suka gabata, Sin ta sanya hannu kan takardun hadin gwiwa  har 34, da kasashen Afirka 19 da ma wasu hukumomi.

Tang ya kara da cewa, Sin ta gina cibiyoyin gwaji na raya fasahohin noma har 24 a sassan Afirka, wadanda suka amfani manoman nahiyar sama da miliyan guda. Kaza lika a bana, ana hasashen cinikayya a fannin albarkatun noma tsakanin Sin da kasashen Afirka, za ta haura dalar Amurka biliyan 10.

A nasa tsokaci kuwa, ministan noma da raya kauyuka na kasar Senegal Samba Ndiobena Ka, cewa ya yi nahiyar Afirka dake hadin gwiwar gudanar da dandalin na FOCAC, na fatan Sin za ta kara zuba jari a fannin samar da na’urorin noma, da sauran abubuwan more rayuwa da ake bukata a nahiyar Afirka.

A shekaru masu zuwa, Sin za ta tallafawa kasashen Afirka wajen kaiwa ga cimma burin su na zamanantar da fannin noma, bisa shirin da aka fitar yayin dandalin.   (Saminu Alhassan)