logo

HAUSA

Xi ya aike da wasikar taya murna ga taron shekara-shekara na 'yan kasuwan mashigin Taiwan

2023-11-14 13:52:22 CMG Hausa

Shugaba Xi Jinping, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS, ya aike da wasikar taya murna ga taron kolin shekara-shekara na 'yan kasuwan mashigin Taiwan na 2023.

Taron wanda aka bude a ranar Talata a birnin Nanjing na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, shi ne ya cika shekara 10 da fara taron kolin 'yan kasuwa na mashigin teku.